Siriya: Hari ya halaka dan Jamus mai da′awar jihadi | Labarai | DW | 19.01.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Siriya: Hari ya halaka dan Jamus mai da'awar jihadi

Denis Cuspert da aka haifa a birnin Berlin na kasar Jamus mawakin zamani ne da ya rikide zuwa yada manufofin mazhabar Salafiyya tare da shiga yaki a Iraki kafin daga bisani ya koma Siriya da sunan yin Jihadi.

Wata kafar yada labarai ta masu da'awar jihadi a Siriya ce ta sanar da mutuwar Denis Cuspert. Dan jihadin da aka fi sani da Deso Dogg a baya a fagen salon kida da waka na zamani na Hip-Hop kafin ya rikide zuwa mai  da'awar jihadi karkashin inuwar kungiyar IS, ya fafata a yakin kasar Iraki a bangaren masu tsatsauran ra'ayin Musulunci na kungiyar IS, karkashin sunan Abu Talha al-Almani kafin ya koma Siriya inda nan ne ya gamu da ajalinsa a farkon wannan makon kamar yadda kafar yada labaran ta tabbatar. Jaridar ta yada hotunan gawar dan jihadin a shafinta inda ta ce ya mutu ne a wani hari da aka kai a yankin Deir al-Zour da ke a gabashin kasar ta Siriya.

Daman can baya,  Amirka da Majalisar Dinkin Duniya sun sanya sunan mutumin mai shekaru 42 cikin jerin 'yan ta'adda da ke barazanar ga tsaron al'ummar duniya.