1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Siriya: Labaran bogi na rura wutar rikici

Ahmed Salisu MNA
July 14, 2018

Masu fafutukar ganin sahihan labarai sun isa ga masu sauraro sun koka kan yadda wani bangare na al'umma ke amfani da labaran da ba su da tushe wajen ruruta wutar rikicin kasar Siriya.

https://p.dw.com/p/31RTU
Symbolbild Europa & Fake News
Hoto: picture-alliance/dpa/M. Murat

Wani dan jarida mai suna Ahmad Primo dan asalin kasar Siriya da ya kafa kungiyar nan ta Verify-sy da ke aiki wajen tabbatar da sahihancin labarai da rahotanni ya ce dabi'ar yada labarai na karya a shafukan sada zumunta na intanet ba za ta amfanawa kasar da ma duniya komai ba illa cigaba da haifar da tashin hankali.

Wannan ne ma ya sanya Mr. Primo din yin kira ga takwarorinsa 'yan jaridu da su tashi haikan wajen magance wannan dabi'a ta hanyar tantance labarai kafin su kai ga yada shi, hakan inji shi, shi ne zai kai ga kawo karshen matsalar fidda labaran bogi da yanzu haka ta zama ruwan dare.