Siriya: Amfani da guba a yakin basasa | Siyasa | DW | 27.11.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Siriya: Amfani da guba a yakin basasa

Masu gabatar da kara na gwamnatin Jamus suna duba shaidun aikata laifukan yaki ta hanyar amfani da sinadarai masu guba a yakin basasar da ake yi a kasar Siriya.

Soldaten der syrischen Regierungsarmee im Dienst in Al-Quneitra

Wani sojan da ke biyayya ga gwamnati Siriya

Makaman roka da aka harba a wannan dare na 21 ga watan Agustan 2013 sun zama masu kara ta musamman da suka far ma yankin da ke hannun masu adawa da gwamnatin Shugaba Bahsar Assad ta Siriya. Makaman da suka fadi a gabashin Ghouta sun tarwatsa gine-gine gami da halaka mutane. An sauya sunayen shaidun saboda dalilai na tsaro, Malama Eman F. ta kasance malamar jinya a asibiti kuma uwa mai 'ya'ya uku wadda ta shaida abin da ya faru lokacin. Ta ce "Kamar ranar karshe, mutane suna mutuwa kamar kiyashi an fesa maganin kwari. Mutane da yawa sun mutu kan tituna, motoci sun tsaya mutane suna dankare a ciki, kamar wadanda suka mutu suna neman tserewa." Wannan sinadarin guba na "Sarin" ba ya da kala ko kamshi kuma tuni ya lalata hanyar da numfashi ke bi. Galibi mutanen da suka shaka kan mutu.

Karin Bayani: Shekaru 20 na shugabancin Assad

Bildergalerie Jahresrückblick 2018

Hare hare sun tsawaita a yakin Siriya

A farkon watan Oktoba wasu kungiyoyi uku masu zaman kansu suka shigar da koke abin da ya faru ga ofishin babban mai gabatar da kara na gwamnatin Jamus, kan hare-haren na makamai masu guba na shekara ta 2013 a Ghouta da 2017 a Khan Shaykhoun. Abin da suke bukata a fayyace yake. A bisa manunfa a shekara ta 2002 Jamus ta kaddamar da tsarin shari'a na bai daya da ya shafi laifuka na kasa da kasa, kamar laifukan yaki da kisan kare dangi. Ofishin mai kabatar da kara ya tabbatar wa DW shigar da koken. Sai dai bai yi karin haske ba.

Karin Bayani: Fargabar amfani da miyagun makami a lardin Idlib

Steve Kostas masanin shari'a ne da ke aiki da daya daga cikin kungiyoyin mai neman tabbatar da adalci da ake kira Society Justice Initiative ya bayyana wasu muhimman kalamu yana mai cewa "Muna da shaida cewa Shugaba Assad yana hannu wajen ba da umurnin. Ban zan ce mu da kanmu za mu iya tabbatar da haka ba, amma muna da yakinin bayanai da suka nuna hannunsa a harin ga gas mai guba."

Syrien Bashar Al-Assad 1999

Bashar al-Assad shugaban kasar Siriya

Bayanan da shaidu suka bayar ya nuna Shagaba Bashar Assad na Siriya kadai yake da ikon ba da umurnin bisa makamai masu guba. A cikin wasu bayanai da tashar DW ta gani an yi imanin Shugaba Assad ya bai wa dan uwansa Maher Assad umurnin amfanin na sinadarin mai guba. Jamus za ta iya samun wadanda suka ba da umurnin da laifi, kuma a bisa dokokin na Jamus wadanda suke da ikon tafiyar da lamura kadai za a tuhuma.