Shugabar gwamnatin Jamus ta bayyana ra′ayinta a taron G7 | Labarai | DW | 26.08.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugabar gwamnatin Jamus ta bayyana ra'ayinta a taron G7

A wannan Litinin ce Shugabannin kasashe masu karfin tattalin arziki ke kammala taron kolinsu a Faransa, inda suke mayar da hankali kan batun gobarar daji a Brazil da kuma kare muhalli.

A daidai lokaci da ake kammala taron kolin shugabannin kasashe masu karfin tattalin arziki a kasar Faransa a wannan Litinin, mahalarta taron sun cika da mamakin zuwan ministan harkokin wajen kasar Iran Mohammad Javad Zarif yayin da suke tsaka da laluben hanyoyin kawo karshen rikici tsakanin Iran da Amirka.

Ministan ya bayyana batun makaman nukiliya a matsayin dalilinsa na halartar taron kolin kungiyar ta G7 ba tare da an gayyato shi ba.

Da take tsokaci game da ziyarar bazatan, shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta bayyana yunkurin kawo karshen rikici da Iran a matsayin abin da ya dace.