1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugabannin yankin Balkans sun je Kiev

Abdourahamane Hassane
April 13, 2022

Shugabannin kasashen yankin Balkans guda hudu sun isa birnin Kiev cikin jirgin kasa domin jadada goyon bayansu ga shugaba Volodymyr Zelensky a yakin da kasarsa take yi da Rasha.

https://p.dw.com/p/49tkB
Polen | Präsidenten von Polen und der baltischen Länder reisen in die Ukraine
Hoto: Office of the President of the Republic of Lithuania/REUTERS

Wannan ita ce ziyara ta biyu da wasu shugabannin yankin na Balkans ke kai wa a Ukraine da nufin nuna goyon bayansu. Shugaban Kasar Jamus Frank-Walter Steinmeier da ke ziyara a birnin Warsaw na Poland ya so tare da shugabannin kasashen na yankin Balkans su kai ziyarar a Kiev amma sai dai shugaban na Ukraine ya ki amincewa. Saboda zargin da ya yi masa na kawo cikas wajen shigar Ukraine cikin kungiyar tarrayar Turai a lokacin da yake rike da matsayin ministan harkokin wajen Jamus.