Shugabannin za su hadu a Masar a kan Zirin Gaza
October 12, 2025
Shugabanni daga sassan duniya na shirye-shiryen halartar babban taron koli kan zaman lafiyar Zirin Gaza, wanda zai gudana a ranar Litinin a birnin Sharm el-Sheikh, na tekun Bahar Maliya na Masar.
Shugaban Masar Abdel Fattah al-Sisi da shugaban Amurka Donald Trump, su ne za su jagoranci taron.
Shugabanni sama da ashirin daga kasashe daban-daban ne ake sa ran halartarsu, ciki har da Sakataren Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres, da Firaministan Burtaniya Keir Starmer da takwaransa ta Italiya Giorgia Meloni da ma Pedro Sanchez na Spain.
Sauran mahalarta sun hada da Shugaban Faransa Emmanuel Macron, Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan, Sarkin Jordan Abdullah na II, da wakilin Tarayyar Turai Antonio Costa.
Fadar shugaban kasa Masar ta ce manufar taron ita ce kawo karshen yakin Gaza, da karfafa yunkurin samar da kwanciyar hankali a yankin Gabashin Tsakiya.