1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU na taro kan makomar Birtaniya

Yusuf Bala Nayaya
October 17, 2018

Shugabanni daga Kungiyar Tarayyar Turai na ganawa a birnin Brussels a ranar Laraba don tattauna batun fitar Birtaniya daga kungiyar EU, abin da ke zuwa bayan kiki-kaka ta ki karewa tsakanin bangarorin biyu.

https://p.dw.com/p/36j2F
Belgien | Beginn EU-Gipfel mit Beratungen zum Brexit
Hoto: Reuters/Y. Herman

Shugabannin na EU sun yi kalamai mabambamta lokacin da suke isa wajen taron na Brussels. A cewar Sebastian Kurz shugaban gwamnatin Ostiriya ba sa tsammanin cimma wata gagarumar nasara sai dai 'yan makonni ko watanni da ke tafe. Ita kuwa Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel cewa ta yi Jamus na cikin shiri ko da an gaza cimma yarjejeniyar da Birtaniya.

Ita kuwa Firaministar ta Birtaniya ta fada wa manema labarai cewa cike take da fata na cimma wasu matakai ga batun na ficewar kasarta daga EU da ma hulda da za su kulla. A cewar May batun da ake takaddama a kansa na iyakar Ireland za su tabo shi inda kuma take da fata za su cimma matsaya.