Shugabanni sun halarci Jana′izar Kofi Annan | Labarai | DW | 13.09.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugabanni sun halarci Jana'izar Kofi Annan

Manyan shugabannin duniya sun halarci jana'izar tsohon magatakardar Majalisar Dinkin Duniya Kofi Annan a wannan Alhamis a kasar Ghana.

Marigayin dan asalin birnin Kumasi na yankin Ashanti dake kudancin kasar ta Ghana, ya sadaukar da rayuwar sa wajen hidimta wa al'umma a Majalisar Dinkin Duniya. Jim kadan bayan binne shi, matarsa Nane Maria ta bayyana shi a matsayin Gwarzo mai juriyar da za a jima ba a mayar da madadin sa ba.

Za a cigaba da tuna marigayin a matsayin bakar fata na farko da ya rike wannan mukami tsakanin shekarar 1997 zuwa 2006. Annan ya rasu ranar 18 ga watan Agusta yana da shekaru 80, bayan gajeriyar jinya da ya yi a kasar Switzerland.