Shugabanni a Kataloniya za su kai kara MDD | Labarai | DW | 01.02.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugabanni a Kataloniya za su kai kara MDD

A cewar lauyansu Ben Emmerson tsarewar da mahukuntan kasar Spain suka yi masu an tsarata ne don hana masu dama ta shiga harkokin siyasa.

Spanien Sitzung des katalanischen Parlaments in Barcelona (Reuters/A. Gea)

Zaman majalisa a yankin Kataloniya

Shugabanni uku daga yankin Kataloniya da aka dauresu a Spain sakamakon shigarsu dambaruwar siyasar yankin a kokarin ballewa daga kasar Spain sun bayyana cewa za su kai kukansu ga 'yan fafutika na Majalisar Dinkin Duniya kamar yadda lauyansu a birnin London ya bayyana a wannan rana ta Alhamis.

A cewar lauyansu Ben Emmerson tsarewar da mahukuntan kasar Spain suka yi masu an tsarata ne don hana masu dama ta shiga harkokin siyasa a matsayinsu na wakilan al'ummar yankin Kataloniya. Lauya Emmerson ya bayyana haka ne a wani taron manema labarai da ya kira a wannan rana.