Shugaban Zimbabwe ya yi jawabi ga majalisar dokoki | Labarai | DW | 15.09.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaban Zimbabwe ya yi jawabi ga majalisar dokoki

'Yan adawa sun yi yunkurin janyo cikas lokacin da shugaban Zimbabuwe Robert Mugabe yake jawabi a majalisar dokokin kasar.

Kofofin yada labaran gwamnatin Zimbabuwe sun katse watsa shirye-shirye kai tsaye lokacin da Shugaba Robert Mugabe yake jawabi ga majalisar dokokin kasar, saboda 'yan adawa sun yi barazanar janyo cikas. 'Yan adawa sun yi ihu lokacin da Mugabe yake shirin fara jawabin saboda sukurkucewar tattalin arziki.

Wani mamba daga bangaren 'yan adawa ya yi zargin cewa an yi musu barazanar kisa idan suka kawo cikas lokacin da Shugaba Mugabe yake jawabi a wannan Talata. Yayin jawabin na mintoci 25 Shugaba Robert Mugabe na kasar ta Zimbabbuwe ya yi alkawarin karfafa hulda da kasashe masu bai wa kasar rance, sannan ya ce za a sassauta dokoki zuba jari saboda janyo masu zuba jari daga kasashen ketare.