Shugaban Yuganda ya bayyana shirin yin tazarce | Labarai | DW | 31.07.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaban Yuganda ya bayyana shirin yin tazarce

Bayan shekaru kusan talatin a kan mulki shugaba Yoweri Museveni na cewa idan an zabe shi zai maida kasar ta Yuganda ta zama ta masu matsakaicin kudaden shiga.

Uganda Präsident Yoweri Museveni

Shugaba Yoweri Museveni na Yuganda

Shugaban kasar Yuganda da ke zama shugaba da ya dade a kan mulkin wannan kasa ya bayyana aniyarsa ta neman a sake zabensa a shekarar 2016, inda ya ce ya samu goyon bayan al'umma kan ci gaba da mulkin wannan kasa tun daga shekarar 1986.

Shugaba Yoweri Museveni ya bayyana cewa yana so ya sauya kasar tasa ta zama mai al'umma masu matsakaicin kudaden shiga.

Sai dai neman bukatar tazarcen ta shugaba Museveni na zuwa ne bayan da Amama Mbabazi tsohon firaministan kasar ke cewa tsarin da kasar ke tafiya a kansa ba na demokradiyya ba ne.