Shugaban Yemen ya ce harin ranar Juma′a na iya rikita kasar | Labarai | DW | 21.03.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaban Yemen ya ce harin ranar Juma'a na iya rikita kasar

Shugaban kasar Yemen ya ce hare-haren da suka halaka rayukan mutane 142 jiya Juma'a a kasar, wani yunkuri ne na tsunduma kasar cikin fadace-fadace.

Shugaban kasar Yemen Abd Rab Mansour Hadi, ya ce hare-haren kunar bakin wake da suka halaka rayukan mutane 142 jiya Juma'a a kasar, wani yunkuri ne na tsunduma kasar cikin fadace-fadace.

Kungiyar nan da ke fafutukar kafa daukar Islama ta IS dai ta dauki alhakin hare-haren da aka kai kan masallatai biyu a babban birnin kasar Sanaa da kuma harin yankin Saada da Houtawan ke da karfi.

Cikin wata wasikar jaje ga iyalan wadanda lamarin ya shafa, ciki har da mutane 351 da suka jikkata, shugaban na Yemen ya ce wannan hari na daga cikin mafiya muni da 'yan ta'addan suka kaddamar a kasar.

Shugaba Abd Rab Mansour dai na fakewa ne a birnin Aden da ke kudancin kasar, bayan tserewa daga daurin talalan da 'yan tawayen su ka yi masa a watan jiya.

Kashe-kashen farko kenan da kungiyar IS ta dauki alhakin kaddamarwa a kasar, kuma wani nuna karfi ne yanzu a yankin da ke da kungiya kamar Al qaida da ke fafutuka a cikinsa.