1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Shugaban Tunisiya ya sake tsayawa takara

Suleiman Babayo ATB
August 6, 2024

Shugaba Kais Saied na kasar Tunisiya ya cika takardar sake takara na neman shugabancin kasar a wani sabon wa'adin mulki yayin da ake shirin gudanar da zabe a watan Nuwamba.

https://p.dw.com/p/4jAbb
Tunesiya | Shugaba Kais Saied
Shugaba Kais Saied na kasar TunisiyaHoto: Chokri Mahjoub/ZUMA Wire/IMAGO

Shugaba Kais Saied na kasar Tunisiya ya cika takardun sake tsayawa takara a zaben shugaban kasa da za a gudanar a watan Oktoba mai zuwa, inda ake sa ran babu wata turjiya mai karfi da zai fuskanta sakamakon matakin kama jiga-jigan 'yan adawa na kasar.

Karin Bayani: Kotu a Tunisiya ta daure 'yar takarar shugaban kasa

Akwai wasu 'yan takara hudu da suka cike takardunsu ciki har da Abir Moussi wadda ta yi kaurin suna wajen caccakar shugaban kuma wadda take tsare tun shekarar da ta gabata, inda yanzu haka aka yanke mata hukuncin daurin shekaru biyu a gidan fursuna, lamarin da ke tabbatar da haramta mata takara a zaben.

Ranar shida ga watan Oktoba mai zuwa ake zaben shugaban kasar ta Tunisiya da ke yankin Arewacin Afirka, yayin da kasar karkashin jagoancin Shugaba Kais Saied take koma salon mulkin kama-karya gabanin juyin-juya halin shekara ta 2011 da ya kawo karshen gwamnatin Marigayi Zine El Abidine Ben Ali.