1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotu a Tunisiya ta daure 'yar takarar shugaban kasa

August 6, 2024

Wata kotu a Tunisiya ta yanke wa wata fitacciyar 'yar adawa da ke takarar shugaban kasa Abir Moussi hukuncin daurin shekaru biyu a gidan kaso bisa samun ta da laifin zagin hukumar zaben kasar.

https://p.dw.com/p/4j9F3
Hoto: Chedly Ben Ibrahim/NurPhoto/picture alliance

Kafin wannan hukuncin da aka yanke shi a ranar Litinin da daddare, Abir Moussi, na cikin'yan takarar zaben shugaban kasa da aka tsara gudanarwa a ranar 6 ga watan Oktoba mai zuwa a Tunisiya. Da ma dai akwai wasu 'yan takarar shugaban kasa guda hudu da su ma wata kotu a Tunisiyan ta yanke musu hukuncin daurin watanni takwas tare da haramta musu tsayawa takara.

Wadannan hukunce-hukunce kan 'yan adawa ne suka kara tayar da zarge-zargen da ake wa shugaba Kais Saied na mulkin danniya ta hanyar amfani da rigar dimukuradiyya da ta kawo shi mulkin kasar a shekarar 2019 amma daga bisani ya rusa majalisa ya koma yana mulkar kasar ta hanyar dokokin ''decree'' irin na soja.