Shugaban Sudan ya bayyana shirin sakin fursunonin siyasa
April 1, 2013Talla
Shugaban gamayyan jam'iyyun adawan kasar ta Sudan guda 20, Farouk Abu Issa ya ce, wannan gagarumin mataki ne na tattauanawa da kawo ci gaba.
Shugaban kasar ta Sudan Omar al-Bashir ya bayyana shirin sakin daukacin fursunonin siyasa, matakin da 'yan adawa su ka yi lale-maraba da shi, wannan yayin da kasar ta rage zaman tankiya da makwabciyarta Sudan ta Kudu.
Lokacin jawabin bude zaman majalisar dokoki da ke birnin Khartoum, shugaban ya ce, za a saki daukacin fursunonin na siyasa ba tare da wani jinkiri ba, cikin matakan da ake dauka na sasantawa.
Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Usman Shehu Usman