1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kungiyar Taliban ta tabbatar da mutuwar Jalaluddin Haqqani

Ramatu Garba Baba
September 4, 2018

Kungiyar Taliban ta tabbatar da mutuwar Jalaluddin Haqqani, shugaban kungiyar nan ta masu kaifin ra'ayin addinin Islama a kasar Afganistan, Jagoran ya mutu ne bayan ya sha fama da rashin lafiya inji sanarwar.

https://p.dw.com/p/34Fig
Jalaluddin Haqqani Netzwerk Terrorismus Pakistan Flash-Galerie
Hoto: AP

Karkashin jagorancin shugaban na Haqqani, mayakan kungiyar sun kai munannan hare-hare na kunar bakin wake da suka janyo asarar daruruwan rayuka, hakazalika kungiyar ta yi kaurin suna a kisan manyan jami'an gwamnatin Kabul da kuma yin garkuwa da turawa don neman kudin fansa.

Wannan dai ba shi bane karon farko da ake fidda sanarwar mutuwar jagoran kungiyar. Yanzu dai rahotannin na cewa dan jagoran mai suna Sirajudin Haqqani ya maye gurbin mahaifinsa. Jalaludin Haqqani abokin kawance ne na kungiyar al-Qaida da kuma kungiyar Taliban.