Shugaban kasar Burundi ya yi rantsuwar kama aiki
August 20, 2015Talla
An rantsar da shugaban kasar Burundi Pierre Nkurunziza a wani sabon wa'adi na uku, bayan da ya lashe zaben da aka gudanar a kasar mai cike da cece-kuce zaben da 'yan adawar kasar suka kaurace masa. An rantsar da shugaban na Burundi ne ya yin wani kware-kwaran biki da aka shirya a takaitaccen lokaci bisa dalillai na tsaro, wanda kuma kasashen duniya basu halarta ba. Kamar dai yadda dokokin kasar suka tanada, an rantsar da shugaban ne a gaban kotun tsarin mulkin kasar, da kuma 'yan majalisun dokokin kasar inda ya yi rantsuwar yin biyayya ga kundin tsarin mulkin kasar, tare da hada kan 'yan kasar da a halin yanzu take fama da tashe-tashen hankulla.