Shugaban Iran ya sha rantsuwar kama aiki | Labarai | DW | 05.08.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaban Iran ya sha rantsuwar kama aiki

Ebrahim Raisi sabon shugaban kasar na Iran ya sha rantsuwar kama aiki ne a gaban majalisar dokokin kasar.

 

Raisi mai tsatsaura ra'ayi wanda ya yi nasara a zaben shugaban kasar da aka gudanar a cikin watan Yunin da ya gabata, wanda 'yan takara da yawa suka kauracewa zaben. Zai mayar da hankali wajen farfado da tattalin arzikin Iran wanda takunkumin karya tattalin arziki da kasashen duniya suka kakabawa kasar saboda shirinta na nukiliya ya durkusar. Magabacinsan Hassan Rohani mai sassaucin ra'ayi, shi ne ya cimma yarjejeniya da kasashen duniyar a kan shirin na nukiliya a shekara ta 2015, kafin daga bisani zuwan gwamnatin Donald Trump, Amirka ta janye daga yarjejeniyar.