Shugaban gwamnatin wucin gadi na Burkina Faso ya koma madafun iko | Labarai | DW | 24.09.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaban gwamnatin wucin gadi na Burkina Faso ya koma madafun iko

Bayan matsin lamba daga kasashen duniya sojojin da suka yi juyin mulki a Burkina Faso sun ajiye madafun iko inda aka sake mayar da gwamnatin rikon kwarya.

Shugaban gwamnatin wucin gadi na kasar Burkina Faso Michel Kafando ya koma kan madafun iko a wannan Laraba da ta gabata, yayin wani karamin biki, mako guda bayan juyin mulkin da sojoji suka yi, wadanda suke da dangantaka da tsohon Shugaba Blaise Compaore.

Jagoran juyin mulkin Janar Gilbert Diendere ya nemi gafara, kuma ya amince da kusruren da ya yi na kifar da gwamnati abin da ya janyo tir daga ciki da wajen kasar. Sojojin kasar ta Burkina Faso da suka jagoranci juyin mulkin sun fuskanci matsin lamba daga kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen yankin yammacin Afirka, ECOWAS, da kuma Faransa wadda ta yi wa kasar mulkin mallaka da sauran kasashen duniya. Tuni Shugaba Kafando ya mayar da gwamnati karkashin Firaminisa Isaac Zida.