1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban Faransa na rangadi a kasar Amirka

Abdullahi Tanko Bala
April 24, 2018

Shugaban Faransa Emmanuel Macron na ziyara a Amirka a wani mataki na karfafa dangantaka tsakanin kasashen biyu.

https://p.dw.com/p/2wY6Y
USA Besuch Präsident Macron und seine Frau
Hoto: Reuters/B. Snyder

Macron yace zai yi amfani da wannan ziyara wajen kokarin shawo kan shugaba Trump domin ci gaba da yarjejeniyar da manyan kasahe shida masu karfin fada aji na duniya suka cimma a 2015 game da shirin nukiliyar Iran, yana mai cewa a halin da ake ciki babu wani tartibin shiri da ake da shi wanda zai maye gurbin yarjejeniyar.

Da take tsokaci mai magana da yawun fadar gwamnatin Amirka Sarah Sanders ta ce shugaba Trump na mai ra'ayin cewa yarjejeniyar ba ta da inganci kuma bai sauya matsayinsa akan batun ba.

Ana sa ran Macron da shugaba Trump za su kuma tattauna akan rikicin Siriya, kasa da makonni biyu bayan da Amirka da Faransa da Birtaniya suka kai hari ta sama kan Siriya a matakin martani ga amfani da makami mai guda da ake zargin gwamnatin Siriyar ta yi wanda ya hallaka mutane da dama a Douma.