shugaban AU ya bukaci yan tawayen Darfur su amince da zaman lafiya | Labarai | DW | 21.05.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

shugaban AU ya bukaci yan tawayen Darfur su amince da zaman lafiya

Shugaban kasar Kongo kuma shugaban kungiyar taraiyar afrika AU, Denis Sassou Nguesso,ya yaba da ci gaba da aka samu dangane da batun samarda zaman lafiya a yankin Darfur na Sudan tare da yin kira ga shugabannin yan tawaye da suka ki sanya hannu a kann yarjejeniyar da su amince da yarjejeniyar.

Shugaban na kasar Kongo ya fadawa manema labarai cewa,sanya hannu kann yarjejeniyar ta Abuja wata nasara ce da kungiyar AU ta samu.

Tun a watan satumba na bara ne shugaban na Kongo ya hango cewa zaa maye gurbin dakarun AU dana majalisar dinkin duniya,kodayake har yanzu baa tabbatar da hakan ba,tunda gwamnatin kasar Sudan tana ci gaba da nuna adawarta game da wannan batu.