Shugaban Amurka yace ya samu ci gaba a dabarunsa kan Iraqi | Labarai | DW | 29.12.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaban Amurka yace ya samu ci gaba a dabarunsa kan Iraqi

Shugaban Amurka George Bush yace ya samu ci gaba mai maana kan sabbin dabaru game da kasar Iraqi.

Shugaban na Amurka ya fadi haka ne a gidan gonarsa dake Texas bayan ganawa da manyan masu bashi shawara, da suka hada da mataimakin shugaban kasa Dick Chaney da sakatariyar harkokin waje Condoleeza Rice da sabon sakataren tsaro Robert Gates.

Ana sa ran Bush zai sanarad sabbin dabarun nasa game da Iraqi a cikin watan janairu mai kamawa.

A halinda ake ciki kuma jamian kasar Amurka sun sanarda cewa suna sa ran a karshen wannan mako ne zaa aiwatar da hukuncin kisa kann tsohon shugaban Iraqi Saddam Hussein.