Shugaban ƙasar Isra´ila ya naɗa Ehud Olmert a matsayin saban Praminista | Labarai | DW | 05.04.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaban ƙasar Isra´ila ya naɗa Ehud Olmert a matsayin saban Praminista

Shugaban kasar Isra´ila Moshe Katsav, ya naɗa Ehud Olmert, Praministan riƙwan ƙwarya, a matsayin saban praminstan da zai girka gwamnati, bayan nasara da jam´iyar sa, ta Kadima ta samu, a zaɓen yan majalisun dokoki, na ranar 28 ga wata maris da ta wuce.

Jim kaɗan, bayan bayyana naɗin sa, Ehud Olmert, ya kiri taron yan majalisar dokoki na jam´iyar sa, inda ya bayyana masu, aniyar sa, ta ci gaba da tantanawa, da sauran jam´iyu, domin girka gwamnatin haɗin kan kasa.

Kamarr yada kudin tsarin mulkin ƙasar Isra´ila ya tanada, Ehud Olmert, na da wa´adin kwanaki 28 ,domin girka wannan gwamnati, idan a tsawan wannan addadi, al´amura su ka cije, ya na da ƙarin kwanaki 14.

A cikin jawabin farko da yayi, bayan naɗin, ya bayyana mahimman batutuwa guda 2, da gwamnatin, zai maida hankali akai.

Wato, batun samar da zaman lahia da Palestinu, sai kuma haɓaka tattalin arzikin ƙasa, da kauttata rayuwar jama´a.