Shugaba Trump ya kaddamar da hari kan Siriya | Labarai | DW | 07.04.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaba Trump ya kaddamar da hari kan Siriya

Wannan dai shi ne karon farko da dakarun na Amirka suka kaddamar da hari kan gwamnatin Siriya kai tsaye bayan da Shugaba Donald Trump ya ba da umarni.

Shugaba Donald Trump na Amirka ya ba da umarnin kaddamar da hari kan dakarun sojan saman Siriya bayan da ake zarginsu da amfani da makami mai guba wajen kai hari da ya yi sanadi na rayukan  mutane da dama da suka hada da yara. Inda shugabanya na Amirka ya ce:

"A wannan rana na ba da umarni a kaddamar da hari kan sansanin sojan kasar Siriya, abu ne da ke da muhimmanci kan makomar tsaron Amirka, kuma abu ne da zai taka birki ga masu amfani da makamai masu guba."

Wannan dai shi ne karon farko da dakarun na Amirka suka kaddamar da hari kan gwamnatin Siriya kai tsaye bayan da Shugaba Donald Trump ya ba da umarni ga dakarun Amirka da ke da sansani a yankin Meditireniya su harba makamai masu linzami, umarnin da ke zuwa sama da watanni biyu da hawan shugaban mulki.

A cewar gwamnan birnin Homs na Siriya Talal Barazi ruwan makamai masu linzami da Amirka ta kaddamar a sansanin sojan Siriya na Shayrat ya yi sanadi na rayukan mutane da dama, wani bangare na sansanin na ci da wuta yayin da wasu da dama suka samu raunika, A cewar Barazi duk wani hari a sansanin sojan na Siriya abin Allah wadarai ne. Shi ma mataimakin jakadan Rasha a Majalisar Dinkin Duniya Vladimir Safronkov alhakin kai wannan hari ya rataya kan wadanda suka assasa harin da ya jawo rasa rayukan wadanda ba su ji ba, ba su gani ba.