Shugaba Rouhani na Iran ya sha alwashin martaba alkawura | Labarai | DW | 04.04.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaba Rouhani na Iran ya sha alwashin martaba alkawura

A cewar shugaban wannan matsaya da aka cimma matsaya ce mai ɗinbin tarihi da za ta buɗe sabon shafin a dangantakar ƙasar ta Iran da sauran ƙasashen duniya.

Shugaba Hassan Rouhani na ƙasar Iran ya yi jawabi ta kafar talabijin inda ya ke bayyana cewa kasar za ta martaba yarjejeniyoyin da aka ƙulla kan shirinta na makamashin nukiliya.An dai bayyana amincewa da shirin mallakar makamashin na nukiliya a ƙasar ta Iran a ranar Alhamis bayan da ƙasashe manya shida suka zauna a ƙasar Switzerland inda suka cimma wata matsaya .A cewar shugaba Rouhani wannan matsaya da aka cimma matsaya ce mai ɗinbin tarihi da za ta buɗe sabon shafi a dangantakar ƙasar ta Iran da sauran ƙasashen duniya.

"Duk wani abu da muka fadawa duniya ko za mu fada za mu tsaya a kansa, duniya ta sani ba ma yaudara abu da ke da muhimmanci shi ne kowane ɓangare ya mutunta abin da muka tsaya a kansa "

Shugaba Rouhani ya ƙara da cewar yarjejeniyar da aka ƙulla mai ɗinbin tarihi za ta sanya ƙasar ta Iran ta rage irin ɓurin da take da shi a fannin na ƙere-ƙeren nukiliya, abin da zai sanya ƙasashen yamma su sassauta ƙan irin takunkumin da aka ƙaƙabawa ƙasar.