Shugaba Rohani ya lashe zaben Iran | Labarai | DW | 20.05.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaba Rohani ya lashe zaben Iran

Mutane miliyan 56 ne dai a kasar ta Iran suka cancanci kada kuri'a a zaben da ake kallo a matsayin zakaran gwajin dafi ga ci gaban gwamnatin shugaba Rohani mai ra'ayin kawo sauyi.

Shugaba mai ci a gwamnatin kasar Iran ya lashe zaben kasar bayan samun yawan kuri'u da suka kasance kashi 58 cikin dari a sakamakon zaben kamar yadda ma'aikatar da ke lura da harkokin cikin gida ta bayyana. Shugaba Rohani mai ra'ayin sauyi dan shekaru 68 da ya jagoranci shirin nukiliyar Iran da ya samu amintar kasashen yammancin duniya. Babban dan adawa da ya fuskanci Rohani dai cikin 'yan takara hudu na zama Ebrahim Raisi mai ra'ayin mazan jiya malami kuma lauya.