Shugaba Obama ya ce dole a dau fansa kan dan jarida James Foley. | Labarai | DW | 26.08.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaba Obama ya ce dole a dau fansa kan dan jarida James Foley.

Amirka ta bayyana cewa dole wadanda suka kashe dan jaridar Amirka James Foley su gurfana a gaban kuliya, ko da kuwa abin zai dau tsawon lokaci.

Shugaba Barack Obama na Amirka ya bayyana cewa ba za su mantaba kuma a shirye Amirka ta ke ta tabbatar da ganin cewa wadanda suke da hannu wajen kisan dan jaridar nan na Amirka da aka yiwa kisan gilla.

Shugaban ya ce har yanzu al'ummar kasar Amirka suna ci gaba da juyayin kisan da mayakan IS suka yi wa James Foley a makon da ya gabata. Shugaba Obama ya kira wadanda su ka yi wannan kisa a matsayin marasa imanin 'yan ta'adda, sai dai shugaban ya nunar da cewa mai yiwuwa a dauki lokaci kafin hukunta masu laifin domin "kawar kawar da cutar daji kamar ta mayakan IS ba abune mai sauki ba, kuma abin zai dauki lokaci " sai dai acewarsa Amirka za ta bi a hankali wajen ganin an yi adalci kan wannan lamari.

Mawallafi: Yusuf Bala
Edita: Abdourrahamane Hassane