Shugaba Mugabe ya yi Murabus | Labarai | DW | 21.11.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaba Mugabe ya yi Murabus

Shugaban kasar Zimbabuwe Robert Mugabe ya mika wa majalisar dokoki takardar yin murabus din sa nan take, kakakin majalisar dokokin Jacob Mudenda ya dakatar da shirin tsige shugaban.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da majalisar ke gabatar da shirin tsige shugaban bayan da jam'iyyarsa ta ZANU-PF ta sanar da cire Mugabe daga shugaban jam'iyya.