1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaba Macron ya sha mari daga matashi

Mouhamadou Awal Balarabe
June 8, 2021

Wani mutun ya sheka wa shugaban Faransa Emmanuel Macron mari a yayin ziyarar da ya kai a yankin kudu maso gabashin kasar, lamarin da ya haifar da fushin dukkan 'yan siyasar kasar.

https://p.dw.com/p/3ubcM
Südafrika Präsident Emmanuel Macron Besuch in Südafrika
Hoto: Siphiwe Sibeko/REUTERS

Dogaran da ke kula da tsaron Emmanuel Macron sun kama wasu matasa biyu 'yan shekaru 28 da haihuwa da ake zargi da aikata da laifin marin shugaban Faransa, in ji ofishin mai gabatar da kara. Shugaban Macron ya ziyarci wata makarantar sakandare na garin Tain-l'hermitage, kafin ya taka zuwa wurin da 'yan garin da suka zo yi masa marhabin da lale, a lokacin da lamarin ya faru. 

Shi dai Mista Macron yana "rangadin yankuna na Faransa"  don sanin zahirin abin da kasa ke ciki bayan fiye da shekara guda da matsalar annobar corona. Shugabannin jam'iyyun siyasa sun yi Allah wadai da abin da ya faru, wanda ya zo a daidai lokacin da zaben shugaban kasa na 2022 ke dada karatowa.