Shugaba Lourenco ya lashe zaben Angola | Labarai | DW | 29.08.2022
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaba Lourenco ya lashe zaben Angola

Jam'iyyar adawa a Angola, ta yi watsi da sakamakon zaben shugaban kasar Angola, wanda hukumar zaben kasar ta tabbatar da nasarar shugaba mai ci.

Hukumar zaben kasar Angola, ta tabbatar da Shugaba Joao Lourenco a matsayin wanda ya lashe zaben shugban kasar da yawan kuri'u kaso 51.17 cikin 100. Wannan nasarar ya ba wa jam'iyya mai mulki ta MPLA damar tsawaita wa'adin mulkin fiye da shekaru 47 da ta fara tun bayan samun 'yancin kai daga aksar Portugal.

Bayan da ya kammala kada kuri'arsa, Shugaba Joao Lourenco yace, "Mun yi amfani da ‘yancinmu na kada kuri'a. Mun ba wa 'yan kasar wannan dama. Kuma a karshe, za mu yi nasara, dimokuradiyya ta yi nasara, Angola kuma ta yi nasara"

Sai dai tuni jam'iyyar adawa a Angola, ta yi watsi da sakamakon zaben da hukumar zaben kasar ta sanar yau a hukumance, tana mai cewa an tafka magudi.