1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban Koriya ta Arewa ya yi bayyanarsa ta farko

Zainab Mohammed Abubakar
May 2, 2020

Shugaba Kim Jong Un na Koriya ta Arewa ya yi fitowarsa ta farko a bainar jama'a bayan kwanaki 20, inda ya jagoranci kaddamar da kamfanin sarrafa taki a kusa da birnin Pyongyang.

https://p.dw.com/p/3bg0t
Nordkorea veröffentlicht neue Bilder von Kim Jong-Un
Hoto: picture-alliance/dpa/KCNA

Wannan ya kawo karshen rade-radin da ake yi dangane da cewar,yana cikin matsanancin yanayi na  rashin lafiya.

Kamfanin dillancin labaru na kasar ta ruwaito shugaba Kim a wajen bukin na Sunchon, tare da wasu jami'an gwamnati ciki har da 'yar uwatrsa Kim Yo Jong, wadda manazarta suka yi hasashen zata maye gurbin dan uwanta, da zarar ya gaza cigaba da mulki.

Jaridun kasar dai sun nuna hoton shugaban na Koriya ta Arewa cikin bakin kaya, yana kewaya harabar kamfanin, kuma babu alamun rashin lafiya a tattare da shi.