1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaba Kim ya isa Rasha

April 24, 2019

Shugaba Kim Jong Un na kasar Koriya ta Arewa, ya isa Rasha yayin da ake shirin ganawa tsakaninsa da Shugaba Vladimir Putin kan batun makamin nukiliya.

https://p.dw.com/p/3HLXb
Russland Nordkorea l Treffen von  Vladimir Putin und Kim Jong Un - Ankunft
Hoto: Reuters/Press Service of Administration of Primorsky Krai/A. Safronov

Mr. Kim ya isa birnin Vladivostok da ke a gabashin Rasha ne cikin wani jirgin kasa don tattauanawa kan batun makaman nukiliyar Koriyar.

A wata hirar da ya yi da tashar Rossiya 24, Shugaba Kim ya kyautata fatan nasara a ganarwarsa da Putin.

To sai dai fa masu nazarin al'amura na cewa Mr. Kim zai nemi goyon bayan Shugaba Putin din ne, bayan ganawar da ya yi da Shugaba Donald Trump na Amirka.

A farkon bana ne shugabannin Koriya da na Amirka suka hadu a birnin Hanoi na kasar Vietnam ba tare da samun daidaito ba.