Shugaba Jonathan ya soke ziyarsa a Chibok | Labarai | DW | 16.05.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaba Jonathan ya soke ziyarsa a Chibok

Da ma dai ziyarar ta shugaban Najeriya ba za ta kasa nasaba da matsin lamba da gwamnmatinsa ke fuskanta ba kan sace 'yan matan sama da wata guda.

Shugaba Goodluck Ebele Jonathan ya soke ziyarar da ya shiya kaiwa garin Chibok da ke jihar Borno, a karon farko sama da wata guda da sace 'yan matan sakandare a yankin. Kasashen duniya da kwararru kan lamura da ka je su zo dai na ci-gaba da sukan gwamnatin Najeriyar da jinkirta martani kan wannan batu, da ma rashin daukar matakan da suka dace na ceto 'yan matan.

Tuni dai Nigeriyar ta amince da tallafin manyan kasashen duniya ciki har da Amurka da Britaniya da Faransa, wajen kubutar da 'yan matan na Chibok.

A yau ne dai Goodluck Ebele Jonathan zai tafi rangadi a kasar Faransa inda zai gana da takwaransa Francois Hollande, domin tattauna halin da Najeriyar ke ciki.

Ana saran wakilan kasasahe da ke makwabtaka da kasar kamar Janhuriyar Benin, da Kamaru da Nijar, za su hade a taron da Faransa za ta dauki nauyin gudanarwa a karshen mako.

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Umaru Aliyu