Shugaba Jonathan ya ce kungiyar Boko Haram barazana ce ga duniya | Labarai | DW | 24.01.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaba Jonathan ya ce kungiyar Boko Haram barazana ce ga duniya

Shugaban Goodluck Jonathan na tarayyar Najeriya ya ce tada kayar bayan 'yan kungiyar nan ta Boko Haram ka iya zama babbar barazana ga sauran kasashen duniya.

Dangane da haka ne ya sa shugaban na Najeriya ya ce dole sai an tashi tsaye domin kawar da wannan matsala

Jonathan ya ambata hakan ne a wata hira da ya yi da gidan talabijin din CNN a jiya Laraba inda ya ce sabanin tunanin da ake da shi, talaucin da ake fama da shi a wasu sassa na kasar bashi da na saba da tada kayar baya ta 'yan kungiyar ta Boko Haram ke yi, kazalika ya yi watsi da zargin da ake yi na cewar soji na cin zarafin mutane a kokarin da su ke na wanzar da doka da oda a sassan da rikicin na Boko Haram ya dabaibaye.

A bisa halin da ake ciki ne dai na rashin tsaro a Najeriyar shugaban ya ce gwamnatinsa ta zage damtse wajen yi aiki da kasashen duniya daban-daban domin ganin an warware wannan kalubale na tsaro.

Shugaba Jonathan ya kara da cewa idan aka bari ana cigaba da yin aiyyuka na ta'addanci a wata kasa to fa ba kasar daya zai shafa ba, zai shafi duniya ce baki daya kuma bai kyautu a rinka sanya siyasa cikin rikicin Boko Haram ba.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Umaru Aliyu