Shugaba Castro bai fito baiyanar jama´a ba a bukin karrama shi | Labarai | DW | 03.12.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaba Castro bai fito baiyanar jama´a ba a bukin karrama shi

An kammala bukukuwan mako guda na girmama shugaban Cuba Fidel Castro ba tare da shugaban ya bayyana a gaban jama´a ba. Ana ganin rashin baiyanarsa da wata alamar cewa Castro bai murmuje daga aikin tiyata da aka yi masa a cikin watan yuli. Dubun dubatan mutane suka hallara a birnin Havana don bukin cika shugaban shekaru 80 da haihuwa wanda kuma yayi daidai da zagayowar shekaru 50 da kaddamar da juyin juya hali da Castro din yayi a kasar ta Cuba. Lokacin da yake jawabi a faretin sojin da aka yi shugaban riko kuma kanin Castro wato Raul Castro ya sake jaddada aniyar gwamnati ta shiga wata tattaunawa da Washington da nufin kawo karshen takunkumin cinikaiya da na tafiye tafiye da Amirka ta kakabawa Cuba.