Shugaba Buhari ya dakatar sakataren gwamnatinsa | Labarai | DW | 19.04.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaba Buhari ya dakatar sakataren gwamnatinsa

Shugaba Buhari ya kuma kafa wani kwamitin mutane uku karkashin mataimakin shugaban kasar domin bincike, su mika rahoto a mokonni biyu.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya dakatar da sakataren gwamnatin kasar Babachir David Lawal da kuma shugaban hukumar tara bayanan sirri Ambassada Ayo Oke da ake zargi cikin wasu jerin badakalar cin hanci.
Shugaba Buhari ya kuma kafa wani kwamitin mutane uku karkashin mataimakin shugaban kasar domin bincike da mika rahoto cikin tsawon makonni biyu.