1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaba Bouteflika zai yi murabus kafin 28 ga watan Afrilu

Mohammad Nasiru Awal ZMA
April 1, 2019

Sai dai bisa ga dukkan alamu matakin da shugaban ya dauka na kafa sabuwar gwamnati bai kai ga gamsar da al'ummar kasar ba.

https://p.dw.com/p/3G37I
Algerien, Algier:  Algerisches Militär fordert Absetzung von Präsident Bouteflika
Hoto: picture alliance/dpa

Fadar shugaban kasar Aljeriya ta fada a wannan Litinin cewa Shugaba Abdelaziz Bouteflika zai yi murabus gabanin cikar wa'adin mulkinsa a ranar 28 ga watan nan na Afrilu. Hakan na zuwa ne bayan da shugaban ya sanar da kafa sabuwar gwamnati karkashin jagorancin Noureddine Bedoui.

Sai dai bisa ga dukkan alamu matakin da shugaban ya dauka bai kai ga gamsar da al'ummar kasar ba. Masu boren kin jinin gwamnati sun ce ba su aminta da sabuwar gwamnatin da ta kunshi ministoci 27 ba, sun kuma sha alawashin ci gaba da zanga-zanga har sai wannan gwamnatin ta yi murabus.

Shugaba Abdelaziz Bouteflika dai ya sanar da kafa gwamnatin rikon kwarya mai ministoci 27, takwas daga cikin ministocin membobi ne na tsohuwar gwamnati da suka yi murabus.

Da farko shugaban ya ba da sanarwar yin murabus dinsa daga gadon mulki a wannan makon don bayar da damar a aiwatar da dokar kundin tsarin mulki ta 102.