Muna amfani da "Cookies" domin inganta abubuwan da muke wallafawa a intanet. Za ku iya samun karin bayani a kundin kare bayananmu.
Cikin shirin za a ji martani daga Najeriya kan aika shugaban 'yan Shi'a gidan yari da kotu ta yi a wannan Alhamis. Akwai ma batun sarkakiyar tsaro a yankin Sahel musamman kyamar da sojojin Faransa ke fuskanta.
Batun yi wa matsalar tsaron kasashen yankin Sahel taron dangi da wahalhalun bakin haure a hamada da kuma yi wa Paul Rusesabagina afuwa, sun dauki hankulan jaridun Jamus a wannan makon.
Galibin jaridun na Jamus din, a wannan makon sun mayar da hankali ne a kan janyewar sojojin Faransa a Mali da kuma yan ta'adda da suka addabi kasar ta Mali.
A wata hira da 'yan jarida, Shugaba Mohamed Bazoum na Nijar ya tabbatar da cewa kasarsa za ta marabci sojojin rundunar Takuba, bayan janyewar dakarun Faransa da na Turai daga Mali.
Kungiyar tattalin arzikin yammacin Afrika ta katse takunkumin da aka kakaba wa Mali watanni shida baya sakamakon jan kafa wajen shirya zabe. Wasu jaridun Jamus sun dubi wannan.