1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

An kamo hanyar warware taddamar nukiliya

Ramatu Garba Baba
April 14, 2021

Amirka da Iran sun kamo hanyar dinke barakar da ke tsakanin kasashen biyu kan shirin nukiliyar Tehran da ake fargabar na tattare da hadarin gaske ga duniya baki daya.

https://p.dw.com/p/3s1wG
Iran Hassan Rouhani und Ali Akbar Salehi
Hoto: Office of the Iranian Presidency/AP Photo/picture alliance

An tsayar da ranar Alhamis mai zuwa a matsayin ranar da Amirka da Iran za su koma kan teburin tattauna yarjejeniyar shirin Nukiliyar ta Iran. Tuni gwamnatin Tehran ta bakin jagoran addinin kasar Ayatollah Ali Khamenei, ta yi kashedi kan duk wani sanda, da ta ce ka iya shafar shirin yin maslahan.

Zaman da za a yi a birnin na Vienna, shi ne zama na farko a tsakanin kasashen biyu, tun bayan da tsohuwar gwamnatin Donald Trump ta fice daga cikin yarjejeniyar da Iran ta cimma da kasashen duniya biyar a shekarar 2015. Ana fargabar shirin nukiliyar Iran na da hadarin gaske amma gwamnatin Tehran ta musanta wannan zargi.