Shirin tsagaita wutar Siriya ya fara aiki | Labarai | DW | 26.10.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shirin tsagaita wutar Siriya ya fara aiki

A yau Juma'a ce shirin tsagaita wuta tsakanin dakarun gwamnatin Siriya da na 'yan tawaye da ke ƙoƙarin kawar da shugaba Bashar al-Assad ya fara aiki a Juma'ar nan.

epa03421206 A handout picture made available on 04 October 2012 by the official Syrian Arab News Agency (SANA) shows Syrian army soldiers during clashes with what SANA claims to be armed terrorist groups at Qudsaya Area, rural Damascus, Syria, 03 October 2012. Government troops and rebels fought fiercely in the northern city of Aleppo, where troops were shelling the districts of Hananu and al-Sakhur, opposition activists said. The violence came a day after at least 31 people were killed in suicide car bombings in Aleppo, Syria_s biggest city and commercial hub. Information coming out of Syria cannot be independently verified, as most foreign media have been barred from restive areas since the uprising against the government of President Bashar al-Assad began in March 2011. EPA/SANA HANDOUT HANDOUT EDITORIAL USE ONLY/NO SALES

Syrien Waffenruhe

Da ya ke magana game da shirin na tsagaita wuta na tsawon kwanaki huɗu, shugaba hukumar kare haƙƙin bani adama nan ta Syrian Observatory for Human Rights da ke da mazauninta a birnin London na Burtaniya, Rami Abdel Rahman ya ce kawo yanzu dai ba su ga alamaun keta wannan yarjejeniya ta tsagaita wuta ba.

A nasu ɓangaren, dakarun gwamnatin Assad sun ce za su mutunta yarjejeniyar to amma fa shakka babu za su maida martani muddin ɓangaren 'yan tawayen su ka keta dokar da aka gindaya.

A farkon wannan makon da mu ke cikin ne dai manzon musamman na Majalisar Ɗinkin Duniya da ƙasahsen larabawa kan rikicin na Siriya Lakhdar Brahimi ya shawarci ɓangarorin biyu da su amince da shirin na tsagaita wuta albarkacin Idin babbar Sallah, kana a yi amfani da damar wajen tattaunawa da nufin wanzar da zaman lafiya a ƙasar.

Mawallafi : Ahmed Salisu
Edita : Mohammed Awal Balarabe