Shirin sanyawa Sudan ta Kudu takunkumi | Labarai | DW | 05.09.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shirin sanyawa Sudan ta Kudu takunkumi

Amirka ta ce ta na shirin kakabawa Sudan ta Kudu takunkumi sakamakon kin mutunta yarjejeniyar da bangarorin da ke rikici da juna a kasar suka yi a kwanakin baya.

Jakadar Amirka da ke Majalisar Dinkin Duniya Samantha Power ta shaidawa kwamitin sulhun Majalisar ta Dinkin Duniya cewa su na shirin kakaba takunkumi kan mutum biyu a Sudan ta Kudu din ne.

Ms Power ta ce mutum guda daga cikin mutanen biyu ya na bangaren gwamnati ne yayin da cikon gudan ke bangaren 'yan tawayen da ke zaman doya da manja da gwamnati shugaba Salva Kiir.

Wannan takunkumi da ake shirin kakabawa dai zai hada da haramta tafiye-tafiye zuwa kasashen duniya da hana taba kadara da kuma haramtawa wanda aka sanyawa din sayen makamai.