Muna amfani da "Cookies" domin inganta abubuwan da muke wallafawa a intanet. Za ku iya samun karin bayani a kundin kare bayananmu.
A cikin shirin za a ji cewa kungiyar Indomitables Lions ta Kamaru ta lallasa takwararta ta kasar Habasha da ci hudu da daya a wasan da suka yi a birnin Yuwunde na gasar cin kofin nahiyar Afirka wato AFCON.
Bayan shekaru 50 Kamaru na karbar bakuncin gasar cin kofin Afirka ta AFCON inda ta ke fatan sake daukar kafin a karo na shida. Sai dai kasar na fatan annobar corona ba za ta dakushe armashin wasannin ba
Mai masaukin baki Kamaru ta lallasa Burkina Faso a wasan farko na gasar cin kofin kwallon kafar Afirka AFCON. Borussia Dortmund ta rage tazarar da ke tsakaninta da Bayern Munich a teburin Bundesliga.
A yayin da ake ci gaba da fafatawa a gasar cin kofin nahiyar Afirka AFCON a Kamaru, kasashe da dama ya zuwa yanzu sun san makomarsu a gasar.
2-1: Wannan shi ne sakamakon nasarar da Kamaru ta samu a kan Burkina Faso a wasan farko na AFCON da shugaban FIFA Gianni Infantino da Shugaba Paul Biya na Kamaru suka halartai a filin wasa mai daukar mutum 60,000.