Shirin rantsar da Shugaba Idriss Deby na Chadi | Siyasa | DW | 20.07.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Shirin rantsar da Shugaba Idriss Deby na Chadi

A lokacin yakin neman zabe Shugaban Idriss Deby Itno na Chadi ya yi alkawarin kawo sauye-sauye a fannoni na siyasa da kundin tsarin mulki da manyan ma'aikatu.

Tschad Präsident Idriss Deby

Shugaba Idriss Deby na kasar Chadi

A ranar a ranar takwas ga wata Augusta ne dai za a rantsar da shugaban na Chadi, wanda ya sha alwashin kawo sauye-sauye a wannan sabon wa'adi na mulki. Sai dai wannan batu bai samu goyon bayan akasarin 'yan kasar ba, musamman ma a bangaran 'yan adawa inda suke zargin Shugaba Deby da kokarin yin amfani da wannan dama domin shigar da tsari na mataimakin shugaban kasa a shugabancin kasar ta Chadi a wani mataki na shirya wanda zai gaje shi. Kuma wannan da na cikin tunanin da Brice Mbaimon Guedmabeye ya ke da shi, wanda shi ne shugaban jam'iyyar MPTR daya daga cikin wadanda suka yi takarar neman shugabancin kasar ta Chadi da shugaba Idriss Deby:

Tschad N'djamena Saleh Kebzabo (L) and Ngarlejy Yorongar

Manyan 'yan adawan kasar Chadi: Saleh Kebzabo da Ngarlejy Yorongar

" Idan batun kawo sauyi a kundin tsarin mulki ya zamanto kokowa ta mutun daya, ai hakan ne ya sa mutane ke zargin cewa shugaban ya na son ne ya sanya wanda zai gaje shi, ko kuma daya daga cikin 'yan gaban goshinsa da ka iya maye gurbinsa nan gaba."

A halin da ake ciki a wannan lokaci, kasar Chadi ba ta bukatar iri-irin wadan nan sauye-sauye a cewar babban jagoran kwamitin da ke kula da sasanta 'yan kasa da samar da zaman Lafiya na kasar ta Chadi Abderamane Ali Gossoumian....

"Mu abun da muke jira a matsayinmu na 'yan kasa, da ke sa'ido a harkokin siyasa, shi ne tsari na garskiya wanda zai bada damar cigaban al'ummar kasar Chadi. A kalla dai kasar ta samu fita daga mugun kangi da take cikinsa yanzu haka. Amma ba wai wasu sauye-sauye na siyasa ba, wanda za a yi su ne kawai domin biyan bukatun 'yan siyasa."

Sai dai tuni cibiyar yada labarai ta jam'iyyar MPS mai mulki a kasar ta Chadi, ta mayar da martani kan wannan zargi, inda ta ce batun wanda zai gaji Shuga Deby ba shi ne burin na sauyin da ake son kawo wa ba, kamar yadda Mahamat Hissein ya yi tsokaci a kai:

Tschad Präsident Idriss Deby Itno - Anhänger im Stadion

Taron jam'iyyar MPS mai mulki a Chadi

"Jam'iyyar MPS ta gane cewa a halin yanzu kan al'ummar kasar Chadi ya waye, kuma shi kan shi shugaban kasa yana da wannan tutani. Kuma yana tsammanin yanzu lokaci ya yi da za a tambayi al'umma domin a ji ta bakinta kan harkokin siyasa da tafiyar da mulkin kasar da ake yi tun daga shekara ta 1990, domin a san irin gyaran da ya kamata a kawo."

Tun dai zaben shugaban kasar da aka yi na kasar Chadi mai cike da cecekuce, wanda ya bai wa shugaba Idriss Deby damar yin tazarce, masu amfani ka da kafofin sadarwa na Internet na fuskantar babban kalubale a kasar, inda basa iya shiga shafuka kamar na Facebook, WhatsApp da Twitter, kuma dalillan ba komai ba ne, illa na siyasa a cewar kungiyar ‘’Internet Sans frontières’’wadda ta ce gwamnati ce ta bai wa kanfanonin sadarwar kasar umarnin takaita shiga shafukan sakamakon rikicin da ya soma kunno kai na bayan zabe.

Sauti da bidiyo akan labarin