A cikin shirin za a ji Firaminista Joseph Dion Ngute na jamhuriyar Kamaru na ci gaba da tattaunawa da bangarori dabam-daban a yunkurin kawo karshen rikicin 'yan aware da na siyasa. Kana a jihar Zamfara da ke Najeriya gwamnati ta yi wani taron manema labarai kan wasu rahotani da suka samu na shirin kitsa kai hare-haren ta'adanci na Boko Haram.