1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shirin mika mulki a Iraqi.

January 7, 2004
https://p.dw.com/p/Bvmj
JAMILU SANI:
A kasar Iraqi yau aka baiyana cewa gwamnatin Amurka ta bada sanarwar yin afuwa ga wasu fursinonin yaki da aka kama zamanin yaki,tare kuma da bada taimako na kudade masi yawa da za'a yi amfani da su wajen harkokin zabe da kuma mika ragamar mulki ga yan asalin kasar ta Iraqi nan da watan Yuni mai zuwa.

Sanarwar data fito daga jami'an gwamnatin Amurka ta baiyana cewa Amurka na duba yiwar nada wani baban jami'in sojin Amurka da za'a dorawa alhakin lura da shirin mika mulki ga yan asalin kasar ta Iraqi,to sai dai kuma wanan mataki da gwamnatin Amurka ke son dauka ya fuskanci kakausan suka daga baban shugban addini na Iraqi.

Ana dai baiyana cewa sanarwar data fito daga ofishin Aytollah Ali al-sistani,shugaban musulmi yan shi'ite na Iraqi ta nuna cewa sabin tsare tsaren da gwamnatin Amurka ke shirin bulo da su da cikin wanan shekara a kasar Iraqi,wanda suka shafi mika mulki ga yan asalin Iraqi abu ne da ba zai taba zaman mai alfanu ga alumar ta Iraqi ba.

Kimanin fursinoni yaki na Iraqi 9,000 ke tsare a haunun sojin Amurka,to sai dai kuma a halin yanzu Amurkan ta ce zata sako fursinoni da yawan su ya kai fiye da 500.

Da yake jawabi ga manema labaru kantoman Amurka a kasar Iraqi Paul Bremer,ya furta cewa sun dauki wanan mataki ne a matsayin wata hanya ta yin sulhu da alumar Iraqi.

Tun a jiya talata gwamnatin shugaba Bush na Amurka ta baiyana cewa ware dola miliyan 458 wajen sake gina Iraqi da kuma shirye shiryen zabe a Iraqi.

A wata kididiga da cibiyar wata cibiyar binciken alamuran duniya ta ADT ta New Yorka ta saba gudanarwa duk shekara,ya nuna cewa kashi 80 daga cikin dari na Amerikawa sun fi mayar da hankalin su ne irin rawar da kafafan yadda labaru na gidajen talbijin ke takawa wajen ilimitar da alumar duniya halin da duniya ke ciki,fiye ma sauran kafofin labaru kamar dai jaridu.

Hakan kuwa ya fito fili ne ta yadda alumar Amurka suka mayar da hankali wajen kalon labarun da suka shafi yakin Iraqi zamanin mulkin saddam Hussien,inda aka baiyana cewa masu kalon akwatunan talbijin miliyan 30 suka rika bin didigin labarun halin da ake ciki a Iraqi.

A wani labarin kuma yau laraba Priministan kasar Holand Jan Peter Balkenede ya kai wata ziyarar aiki ta ba zata kasar Iraqi,don saduwa da dakarun kasar dake zaune a kudancin Iraqi,kamar yadda wanan sanarwar ta fito daga gwamnatin kasar Holand.

Sojin dai na kasar Holanda ya yawan su ya kai 1,100 an girke su ne a lardin Al Muthanna na kudancin Iraqi,yankin kuma dake karkashin kulawar sojin Birtania.

A watan da ya gabata ne dai majalisar dokokin Holand ta amince,a kara wa'adin zaman dakarun kasar dake Iraqi har nan da watan Yuli na wanan shekara da muke ciki.