Shirin Abu Namu ya duba rashin shan romon dimukuradiyya ga mata a Najeriya | Zamantakewa | DW | 03.06.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Shirin Abu Namu ya duba rashin shan romon dimukuradiyya ga mata a Najeriya

A Najeriya matan na korafin cewa ana mantawa da su wajen shan romon dimukuradiyya, duk da yake 'yan siyasa idan zabe ya gabato su kan shiga gida-gida da kauyuka suna rabawa matan atamfofi da sabulai don neman kuri'un matan a gabanin zabe. Sai dai bayan 'yan siyasar sun samu nasarar hayewa kan madafan iko, sukan mayar da matan saniyar ware.

Saurari sauti 09:45

matan kan yi korafin cewa ana mantawa da su musamman ta fuskacin shan romon dimukuradiyya. A Najeriya sau tari 'yan siyasa idan zabe ya gabato su kan shiga kauyuka su rinka rabawa mata atamfofi da sabulai da makamantansu. Su kan shiga gida-gida domin neman kuri'u na matan, sai dai da zarar sun samu nasara, su kan manta da dukkanin alkawuran da suka yi wa matan. Ba ya ga haka, matan kan koka da cewa ba ma a basu damarmakin da dokokin kasa da kasa da ma kundin tsarin mulkin Najeriyar ya ba su, wato adadin kason da aka amince a baiwa mata a mukamai na siyasa da ma na tafiyar da harkokin gwamnati. Sau da dama matan kan koka cewa a kan yi amfani da su a lokutan yakin neman zabe kana a yi musu abin nan da Malam Bahaushe ke cewa an ci moriyar ganga an yasar da kaurenta, kana ba ma a barinsu su taka rawar azo a gani idan batun tsayawa takara ya zo, ma'ana ba a barinsu su fito takarkaru a mukamai da ban-daban ko kuma idan ma har an bar sun a kan tsula kudi na ban mamaki, wanda hakan kan hana su samun damar tsayawa takarar.