Shekaru biyu da juyin mulkin soji a Myanmar | Siyasa | DW | 01.02.2023
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Shekaru biyu da juyin mulkin soji a Myanmar

Kasashen Amirka da Kanada da Birtaniya da Ostiraliya sun sanya takunkumi kan hukumar zaben Myanmar da kamfanonin makamashi da ma'adinai a lokacin da kasar ke cika shekaru biyu da juyin mulki.

Shekaru biyu da juyin mulkin Myanmar

Shekaru biyu da juyin mulkin Myanmar

Shekaru biyu bayan sojoji sun kwace madafun ikon kasar Mynmar ta hanyar juyin mulki, tun lokacin ake samun tashe-tashen hankula irin na yakin basasa. A cikin wannan shekara ta 2023 sojojin suna neman hanyar samun amincewa ta hanyar tsara zaben jeka na-yi-ka. Dubban mutane sun mutu kana wasu fiye da miliyan daya da rabi sun kasance 'yan gudun hijira na cikin gida a wannan yakin basasa da ake fuskanta a kasar ta Myanmar.

Hoton hambararriyar shugaban kasar Aung San Suu Kyi

Hoton hambararriyar shugaban kasar Aung San Suu Kyi

Tun ranar 1 ga watan Febrairun 2021 da sojoji suka kwace madafun iko ake samun hare-hare da garkuwa da mutane a kusan duk daukacin kasar. Gidajen fursunoni suna shake da 'yan siyasa wadaanda ake gallaza musu azaba kana sojojin sun kashe wasu. Tsohuwar Firaminista Aung San Suu Kyi an yanke mata hukuncin daurin fiye da shekaru talatin bayan wata shari'a. Yan jarida a kasar kuwa, suna aiki karkashin mawuyacin yanayi da barazana da kuma cin zarafi har da kisa.

Yan gudun hijirar Myanmar a Indonesiya

Yan gudun hijirar Myanmar a Indonesiya

Masana suna ganin masu nuna turjiya suna yi a wurare daban-daban domin yi wa gwamnatin mulkin sojan matsin lamba da kure irin karfin da sojojin suke da shi, ganin suna ci gaba da samun makamai daga Rasha ga misali.

Rikicin na Myanmar ya shafi tattalin arzikin kasar inda masu nuna tirjiya kan mulkin sojojin ke ci gaba da bin matakan hana gwamnatin samun kudin da take bukawta, wajen kauracewa kamfanonin da suke da hannu a ciki da wasu matakai inda tuni tattalin arzikin kasar ya samu koma baya.

Sauti da bidiyo akan labarin