1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bikin ranar hadin kai karo na 50 a Kamaru

Zakari Sadou ZUD
May 20, 2022

Ana gudanar da kasaitaccen bikin a birnin Yaoundé, shelkwatar kasar ta Kamaru. Sai dai a Bemenda, 'yan aware masu hankoron kafa kasa mai magana da Ingilishi tuni suka gargadi mazauna da kada wanda ya fito a wannan rana.

https://p.dw.com/p/4Bdi8
Kamerun Wahl l Präsident Paul Biya
Hoto: picture alliance/dpa/j. Warnand

Hukumomi a Kamaru na bikin cika shekaru 50 da hadewar kasar a matsayin kasa daya dunkulalliya, bayan da al’ummar kasar ta kada kuri’ar amincewa da hakan a 1972. Duk da cewa an aiwatar da sauye-sauye na siyasa game da yadda ake tafiyar da kasar, to amma daga bisani an sake samun barkewar tashe-tashen hankula musamman masu amfani da turancin Ingilishi, inda 'yan aware ke yunkurin fice daga Kamaru domin su kafa wata kasa da suke wa lakabi da Ambazoniya. Masanin tarihi Uba Ali Mohammed a Kamaru ya yi zargin tun zamanin mulkin tsohon shugaba Ahmadou Ahidjo, lokacin da Kamaru ta dunkule ne aka tafka kurarai. Daga bisani kuma a cewar Mohammed sai gwamnatin Shugaba Paul Biya da ke ci ta kara lalata al'amura.


Tun da farko dai manufar samar da tarayya Kamaru ta zo ne karkashin sha’awar da 'yan kasar suka nuna ta son rayuwa tare, a lokacin da kasar ke karkashin mulkin mallakar kasar Jamus karkashin wata yarjejeniya da Majalisar Dinkin Duniya ta shirya a Kamaru ta Birtaniya inda yankin kudancin kasar ya amince ya hade da yankin gabashi. 

A yanzu dai DW ta fahimci cewa duk da shekaru 50 da Kamaru ta kwashe a matsayin dunkulalliyar kasa, matsalar kabilanci da 'yan aware na yi wa dorewarta a matsayin dunkulalliya barazana.