Shekaru 100 da kisan kiyashi a Armeniya | Siyasa | DW | 24.04.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Shekaru 100 da kisan kiyashi a Armeniya

Al'ummar kasar Armeniya sun gudanar da bikin cika shekara 100 da kisan kimanin mutane miliyan daya da rabi da aka yi wa 'yan kasar a lokutan gushewar daular Turkiya.

Kasar ta Armeniya wacce ta kasance karkashin Tarayyar Sobiyat har zuwa shekarar 1990 da ta samu 'yancin kanta amma har yanzu jami'an tsaron kasar Rasha ke samar mata da tsaro karkashin wata yarjejeniya da za ta kai har shekarar 2045. Celil Ersoglu da ke zama mai rakiya ga masu yawon bude ido kan iyakokin wadannan kasashe ya ce iyakar da ke zama a bude a lokacin yakin cacar baka an rufe ta baki daya har tsawon shekaru 20. Mr. Ersoglu ya ce ''daya bangaren iyakar ta Armeniya gaba daya dakarun Rasha ne ke sanya idanu a kansa kuma ba sa barin kowa ya tsallaka.''

Völkermord an den Armeniern 1915

Mutane da dama ne suka rasu sakamakon kisan kiyashin da aka gudanar a Armeniya

A dai wannan iyaka ta Armaniya rayuwa ta kasance mai wahala saboda rashin kai kawon jama'a abinda ya sa mutanen ma da ke da gidaje da gonaki kauracewa yankin haka batun ya ke a bangaren iyakar ta Turkiya ma, a garin Akyaka da ke da gidaje da aka gina da laka ya kasance tashar jirgin kasa da mutane kan yada zango idan suka fita ko suka dawo za su shiga Turkiya.

A cewar magajin garin na Akyaka da ke iyakar Turkiya Muhammet Toptas lokacin da iyakar na bude akwai jiragen kasa da ke safara tsakanin kasashen biyu akwai yalwa ta kasuwanci amma yanzu kam babu aiki, matasa ba abin yi wanda hakan ke shafar dukkan kasashen biyu. A nasa ra'ayin abin da ya faru a shekarun baya bai kamata ya ci gaba da jawo koma baya ba ga mutanen wannan zamani ba.

Teheran Demonstration von Armeniern 100. Jahrestag Völkmermord

A kasashen duniya da dama an gudanar da bikin tunawa da kisan kiyashin Armeniya

Ko da yake mahukuntan na Turkiya na bayyana cewa yawan wadanda ake cewa sun rasu a Armeniya ba su kai abinda ake fadi ba amma abu ne da ba za a manta da shi ba kasancewar har cikin manhajar karatun dalibai ana halarto wannan tarihi da yanzu ya sanya mutanen musamman da ke iyakokin kasashe cikin rayuwa mai wahala

Kisan kiyashin na shekarar 1915 a Armeniya ya kasance muhimmin bangaren a manhajar karatun dalibai a kasar inda koda a bikin cika shekaru dari na wannan kisan kiyashi, sai da aka kawata makarantar da wasu furanni da ke nuna kada a manta da tarihi.

Sauti da bidiyo akan labarin