1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shekara guda da harin birnin Nice

Ramatu Garba Baba
July 14, 2017

A kasar Faransa an karfafa tsaro a duk fadin kasar a yayin da ake bikin ranar juyin juya halin Bastille da ya zo dai dai da cika shekara guda da kai harin birnin Nice da ya halaka mutane fiye da tamanin

https://p.dw.com/p/2gaNF
Frankreich Nizza Hollande Sarkozy Prinz Albert bei Trauerfeier für Opfer des Anschlags mit LKW
Hoto: Getty Images/AFP/L. Cipriani

A ranar 14 ga watan Yulin bara ne dai wani mahari mai suna Mohamed Bouhlel ya kutsa da wata babbar mota a tsakiyar jama'a inda a cikin mintuna kalilan aka samu asarar rayukan mutane 86 ciki har da kananan yara. Shugaba Emmanuel Macron ya jagoranci sauran al'ummar kasar a taron da aka yi don gudanar da addu'oi da kuma karrama wadanda suka nuna bajinta a lokacin harin.

Daga cikin mutane fiye da dari hudu da suka sami rauni sakamakon harin na birnin Nice, har ya zuwa wannan lokacin akwai wasu da ke gadon asibiti suna jiyar munanan raunin da suka samu. Bincike ya nuna cewa Maharin mai suna Mohammed Bouhlel dan kasar Tunisiya ne da ke da izinin zama a Faransar.

Mahukuntan Faransa na ci gaba da tsare wasu mutane tara da ake zargi da hannu a harin.